"Kamar yadda yake a rubuce cewa, 'Babu wani mai adalci, babu, ko ɗaya'."   Romains 3:10

   "Gama 'yan dam duka sun yi zunubi, sun kasa kuma ga ɗaukakar Jehovah."   Romains 3:23

   "Gama sakamakon zunubi mutuwa ne, amma baiwar Jehovah ita ce rai madawwami a cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu."   Romains 6:23

   "Amma kuwa Jehovah yana tabbatar mana da ƙaunar da yake yi mana, wato tun muna masu zunubi, Almasihu ya mutu dominmu."   Romains 5:8

   "Saboda ƙaunar da Jehovah ya yi wa duniya har ya ba da makaɗaicin Ɗansa, domin duk wanda ya gaskata da shi kada ya hallaka, sai dai ya sami rai madawwami."   Jean 3:16

   In kuwa muka bayyana zunubanmu, to, shi mai alkawari ne, mai adalci kuma, zai kuwa gafarta mana zunubanmu, ya tsarkake mu daga dukkan rashin adalci."   1 Jean 1:9

   "Wato, in kai da bakinka ka bayyana yarda, cewa Yesu Ubangiji ne, ka kuma gaskata a zuciyarka Jehovah ya tashe shi daga matattu, za ka sami ceto.  Domin da zuci mutum yake gaskatawa yă sami adalcin Jehovah, da baki yake shaidawa ya sami ceto."   Romains 10:9-10

   "Amma duk iyakar waɗanda suka karɓe shi, wato, masu gaskatawa da sunansa, ya ba su ikon zama 'ya'yan Jehovah."   Jean 1:12

   "Yesu ya ce masa, “Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba sai ta wurina."   Jean 14:6

   "Yadda Uba yake ta da matattu ya kuma raya su, haka Ɗan ma yake rayar da wanda ya nufa."   Jean 5:21

   "Domin ta wurin alheri ne aka cece ku saboda bangaskiya, wannan kuwa ba ƙoƙarin kanku ba ne, baiwa ce ta Jehovah,  ba kuwa saboda da aikin lada ba, kada wani ya yi fariya."   Éphésiens 2:8-9

   "A yanzu kuma, 'yan'uwa, zan tuna muku da bisharar da na sanar da ku, wadda kuka karɓa, wadda kuke bi, ...  Jawabi mafi muhimmanci da na sanar da ku, shi ne wanda na karɓo, cewa, Almasihu ya mutu domin zunubanmu, kamar yadda Littattafai suka faɗa,  cewa an binne shi, an ta da shi a rana ta uku, kamar yadda Littattafai suka faɗa."   1 Corinthiens 15:1,3-4

   "Saboda haka, sai ku riƙa bayyana wa juna laifofinku, kuna yi wa juna addu'a, don a warkar da ku. Addu'ar mai adalci tana da ƙarfin aiki ƙwarai da gaske."   Jacques 5:16

   "Ya ku ƙaunatattuna, sai mu ƙaunaci juna, domin ƙauna ta Jehovah ce. Duk mai ƙauna kuwa haifaffen Jehovah ne, ya kuma san Jehovah.   Wanda ba ya ƙauna, bai san Jehovah ba sam, domin Jehovah shi ne ƙauna."   1 Jean 4:7-8

   "Don haka, ya ku ƙaunatatuna, da yake kun riga kun san haka, ku kula kada bauɗewar kangararru ta tafi da ku, har ku fāɗi daga matsayinku.  Amma ku ƙaru da alherin Ubangijinmu, Mai Cetonmu Yesu Almasihu da kuma saninsa. Ɗaukaka tă tabbata a gare shi a yanzu, da kuma har abada.  Amin! Amin!"   2 Pierre 3:17-18